IQNA

Yahudawan Na Shirin Aukawa Masallacin Al-aqsa

14:27 - September 15, 2022
Lambar Labari: 3487857
Tehran (IQNA) Yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna na shirin aukawa kan masallacin Al-Aqsa a ranar 29 ga wannan watan Satumba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin labarai na Falastinu sun tabbatar da cewa, Yahudawan sahyuniya ‘yan share wuri zauna na shirin yin kutse mafi girma na tarihi a kan masallacin Al-Aqsa a ranar 29 ga watan Satumba, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekara ta Ibraniyawa.

An buga wannan labarin ne sa'o'i bayan da wasu 'yahudawa da dama suka kutsa kai cikin harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a lokaci guda, tare da kame Falasdinawa da dama da sojojin mamaya suka yi.

Ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta Quds ta sanar da cewa, wasu da dama daga cikin gungun yahudawa da suke karkashin kulawar 'yan sandan sun masallacin Al-Aqsa daga yankin Bab al-Maghraba, inda suka gudanar da ayyuka na tsokana ga musulmi da sunan suna gudanar da  bukukuwan Talmud a Bab -Rahmah da ke cikin harabar masallacin.

A cikin wata sanarwa da cibiyar Quds ta kasa da kasa ta fitar, ta yi kira ga kasashen Larabawa da na Musulunci da su tunkari wadannan ayyuka na tsokana da Isra'ila take shiryawa da sunan bukukuwan Yahudawa.

 

4085663

 

captcha