IQNA

Martanin Hamas game da hankoron dauke ofishin jakadancin Biritaniya zuwa Quds

16:59 - September 23, 2022
Lambar Labari: 3487899
Tehran (IQNA) Hamas kuma ta bayyana yiwuwar mayar da ofishin jakadancin Birtaniya zuwa birnin Kudus a matsayin wani mataki da bai dace ba tare da bayyna haka a matsayin goyon bayan 'yan mamaya da kuma kiyayya ga al'ummar Palastinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hamas ta mayar da martani kan Matakin da Birtaniyya za ta dauka na mayar da ofishinta zuwa Quds, da cewa hakan bai dace ba,  kuma hakan ba zai iya halatta mamayar Isra'ila ba.

Dangane da labarin yiwuwar mayar da ofishin jakadancin Birtaniya zuwa birnin Kudus, Abdul Latif al-Qanou kakakin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu ya bayyana cewa: Sanarwar da Firaministan Birtaniya Liz Truss ta yi dangane da aniyarta ta mayar da ofishin jakadancin kasarta daga Tel Aviv zuwa Kudus wani bangare ne na nuna son kai ga mamayar yahudawan sahyoniya da kuma hada kai da su, da kuma nuna kiyayya da al'ummar Palastinu.

Al-Qanoo yana mai jaddada cewa wannan mataki ba zai iya halalta mamaya ko da wani yanki na kasarmu ba, Al-Qanoo ya kara da cewa: Kudus kasa ce da aka mamaye kuma ta al'ummarmu ce. Mayar da ofishin jakadanci a can ba zai canza gaskiyar ba kuma ba zai canja tarihi ba.

Ya bayyana cewa a ko da yaushe Ingila tana goyon bayan yahudawan sahyoniyawan kuma har yanzu tana goyon bayansu kuma kasar ce ta yi musu alkawarin mika mata kasarmu, ya kuma bayyana cewa, wannan mataki shi ne ci gaba da kiyayya da al'ummarmu da kuma mamaye wuraren ibada na Musulunci da na Kiristanci a birnin Kudus.

 

4087303

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: martani ، Hamas ، yahudanci ، ofishin jakadanci ، Quds
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha