IQNA

An Gano kur'ani mai girma mai shekaru dari biyar a kasar Spain

15:27 - August 20, 2023
Lambar Labari: 3489672
Madrid (IQNA) An gano kwafin kur'ani tare da wasu rubuce-rubuce biyu na farkon ƙarni na 16 a bangon wani tsohon gida a kudancin Spain.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Akhbar cewa, an gano wannan rubutun da wasu kwafi biyu kusa da katangar wani gida a birnin Malaga da ke kudancin kasar Spain. Wadannan rubuce-rubucen na wani malamin fikihu ne mai suna Muhammad al-Jiyar, wanda baya ga fikihu, shi ma malami ne a fannin lissafi, wakoki, da falaki.

A cewar kafofin watsa labarai na Spain, an ɓoye waɗannan rubuce-rubucen fiye da ƙarni 5, amma an gano su a lokacin gyarawa a ranar 28 ga Yuni, 2003, duk da haka, kwanan nan aka buga labarin wannan binciken bayan fiye da shekaru ashirin. .

Al-Giyar malamin fikihu ne kuma mai wa'azi daga birnin Al-kawsar da ke yankin Malaga a kasar Andalusia na wancan lokacin kuma ya shiga wannan gari a shekara ta 1490. A cikin ayyukansa ya yi bayani kan batutuwan fikihu da na tarihi, kuma a cikin wadannan ayyukan ya yi bayanin halin da Andalusiya ke ciki a wannan rana, da kuma faduwar Granada da kuma karshen mulkin musulmi a kasar Spain.

A cikin 1500, sarakunan Kirista sun yarda da shi ya zama Kirista ko kuma ya bar Andalusia, kuma ya zaɓi na biyu; Amma Al-Jiyar duk da barin wannan garin, ya boye Mus'af dinsa da kwafin ayyukansa guda biyu a bangon gidansa da fatan wata rana zai koma birnin.

Mai gidan na yanzu yana cewa game da wannan binciken: Mun yi mamakin samun waɗannan rubuce-rubucen kuma ba wanda ya yi tsammanin faruwar haka, waɗannan rubuce-rubucen an rufe su kuma an ɓoye su a cikin faɗuwar bangon gidajen Andalus na gargajiya.

Maria Isabel Callero, wata ‘yar asalin yankin gabas kuma farfesa a jami’a mai ritaya, wadda ta shafe mafi yawan lokutanta tana nazarin rubutun asali a jami’ar Malaga, ta ce: Wannan Al-Qur’ani na daya daga cikin tsofaffin litattafai biyu da aka gano a kasar Spain.

 

4163441

 

captcha