Wakilin Al-Mayadeen a birnin Damascus ya bayar da rahoton cewa, wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra'ila ya harba makamai masu linzami guda biyu tare da auna wata mota a garin Al-Baath da ke lardin Quneitra, sakamakon haka mutane 4 suka yi shahada.
A cewar wannan rahoto, wannan jirgi mara matuki na Isra'ila ya harba makamai masu linzami guda biyu kan wata mota, inda ya kashe akalla mutane hudu.
A 'yan kwanakin da suka gabata makiya yahudawan sahyoniya sun kai wani hari ta sama daga yankin Golan da suka mamaye tare da kai farmaki kan wasu yankunan da ke kewayen birnin Damascus.
A cikin wannan harin, na'urorin tsaron sararin samaniyar Siriya sun yi nasarar lalata mafi yawan makamai masu linzami na gwamnatin Sahayoniya, kuma fashewar wasu makamai masu linzami ya haifar da hasarar dukiya.