Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Ain cewa, kasar Saudiyya na gabatar da tasbaha ga maniyyata a lokacin gudanar da aikin hajjin bana, wanda ke da ban sha’awa.
Maimakon sanadarin alkahol an yi amfani da ganyen shayi don kashe kwayoyin cuta a ta hanyar amfani da wannan tasbaha.