IQNA

Ci gaba da ayyukan da'irar haddar kur'ani mai tsarki a zirin Gaza

15:12 - June 13, 2024
Lambar Labari: 3491331
IQNA - Duk da ci gaba da yake-yake da kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta yi kan al'ummar yankin zirin Gaza, harda da karatun kur'ani na ci gaba da aiki a wannan yanki da yaki ya daidaita.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Quds Al-Akhbariya cewa, duk da ci gaba da yake-yake da kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta yi wa al'ummar yankin zirin Gaza, da'irar haddar kur'ani mai tsarki a Gaza na ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ma'aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar da sanarwa a jiya, inda ta sanar da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sojojin yahudawan sahyoniya sun yi kisan kiyashi kan iyalan Palasdinawa 3 a zirin Gaza, inda suka yi shahada 40 tare da jikkata wasu 120.

A cewar wannan sanarwa, har yanzu wasu daga cikin wadanda abin ya shafa na karkashin baraguzan gine-gine kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farin kaya ba za su iya isa gare su ba. Adadin wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai ya kai shahidai 37,164 da kuma jikkata 84,832 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yau (kwanaki 239 na yaki).

Halin jin kai a zirin Gaza bayan kwanaki 249 na yakin basasa yana kara ta'azzara a kowace rana a karkashin inuwar mamaye wannan yanki da kuma ci gaba da yakin kamar yadda Antonio Guterres, babban sakataren MDD ya sanar da cewa; Kashi 80% na al'ummar Zirin Gaza na faruwa ne sakamakon ci gaba da yaki da kuma katsewar agajin da ba sa iya samun ruwan sha.

 

 
 

4221174

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yahudawa zirin gaza kisan kiyashi shahada mdd
captcha