IQNA

An bayar da kyautar kwafin kur'ani 60,000 ga alhazan kasar Iraki

15:18 - June 22, 2024
Lambar Labari: 3491383
IQNA - Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci, da'awah da jagoranci ta kasar Saudiyya ta sanar da bayar da kyautar kur'ani mai tsarki 60,000 ga mahajjatan kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sabq cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci, da’awah da shiriya ta kasar Saudiyya ta sanar da bayar da gudunmuwar kur’ani mai tsarki 60,000 ga mahajjatan kasar Iraki.

Wannan kwafin kur’ani mai tsarki, wanda cibiyar sarki Fahad ce ta buga shi, an bayar da shi ne ga alhazan Iraki da ke barin wannan kasa ta mashigar Arar da ke arewacin Saudiyya.

Dangane da kokarin da ake yi na hidimar kur'ani mai tsarki da mahajjatan Baitullahi Ihram, mahajjatan kasar Iraki sun yaba da wannan aiki na ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci da da'awah ta kasar Saudiyya.

A baya ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta Saudiyya ta sanar da cewa, ana ci gaba da shirye-shiryen yi wa maniyyata hidima, musamman wadanda ke shiga Madina da kuma barin Saudiyya ta filayen jiragen sama na birnin.

A cewar wannan ma'aikatar, hadin gwiwa da cibiyar sarki Fahd don buga kur'ani mai tsarki a Madina an  ware fiye da mujalladi dubu 900 na kur'ani ga wannan yanki.

Ana ajiye wadannan kwafin ana rarraba su a wurare a filin jirgin sama na Muhammad Bin Abdulaziz da ke Madina da filin jirgin saman yankin Yarima Abdul Mohsen Bin Abdulaziz da ke Yanbu, kuma an shirya wuraren tashi da saukar jiragen sama na filayen jiragen saman biyu don taimakawa mahajjata da ke barin Saudiyya.

 

4222627

 

 

 

 

captcha