IQNA

Babban Masallacin Kufa Ya Karbi bakuncin Masu ziyarar Arbaeen

14:23 - August 24, 2024
Lambar Labari: 3491748
IQNA – A kowace rana dubun dubatar masu ziyarar Arbaeen ne ke ziyartar babban masallacin Kufa da ke kusa da Najaf.

Babban Masallacin Kufa da ke da tazarar kilomita 12 daga arewacin birnin Najaf na kasar Iraki, yana daya daga cikin manyan masallatai a kasashen musulmi.

Mabiya mzhabar ahlul bait suna daukarsa a matsayin masallaci mafi muhimmanci na hudu bayan Masjid al-Haram, Al-Masjid an-Nabawi, da kuma Masallacin Al-Aqsa.

Masallacin da aka yi imani da cewa Annabi Adam (AS) ne ya gina shi, yana da dimbin tarihi, kuma annabawa da waliyai da dama sun ziyarce shi, ciki har da Annabi Muhammad (SAW), Imam Ali (AS), Imam Hassan (AS), da Imam Hussain (AS), da sauransu. 

Haka nan kuma yana kunshe da kaburburan fitattun mutane irinsu Muslim ibn Aqeel, Hani ibn Urwa, da Al-Mukhtar, kuma kewaye yake yake da wuraren tarihi ciki har da gidan Imam Ali (AS).

 

 

 
 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tarihi birnin najaf muhimmanci masallaci imani
captcha