IQNA

Kwamitin kula da harkokin musulmi a Amurka ya bukaci Trump da ya kawo karshen yakin Gaza

13:41 - November 07, 2024
Lambar Labari: 3492165
IQNA - Kwamitin kula da harkokin musulmi a Amurka ya yi kira ga Donald Trump, wanda ya lashe zaben Amurka, da ya cika alkawarinsa na kawo karshen yakin Gaza.

A bisa rahoton Anatoly, Kwamitin kula da harkokin musulmi a Amurka, ya bukaci zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya ba da fifiko wajen cika alkawarin da ya dauka a yakin neman zaben da ya yi na samar da zaman lafiya a kasashen ketare, ciki har da kawo karshen yakin da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ke yi a zirin Gaza.

Nihad Awad, darektan kwamitin, a wata sanarwa ga jami'an jam'iyyar Democrat, ya jaddada cewa ya kamata su dauki darasi daga rashin goyon bayan Kamla Harris daga masu zabe musulmi, Domin kuwa musulmin Amurka sun nuna adawarsu da kisan gillar da gwamnatin Isra'ila take yi a Gaza ta hanyar kin kada ma Kamala Harris kuri'a.

Wannan kungiya ta bayyana cewa: Muna sa ran dukkan zababbun jami'ai da su kula da gaskiyae lamari,  kuma magance matsalolin musulmi masu jefa kuri'a, kuma wannan bukatar ta shafi shi kansa zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Da yake  nuni da cewa Trump ya yi alkawarin dakatar da zubar da jini a zirin Gaza, ya kara da cewa: Dole ne Trump ya cika alkawarinsa da ya dauka a yakin neman zabensa, da kuma neman zaman lafiya a kasashen waje, gami da kawo karshen yakin Gaza. Amma dole ne wannan zaman lafiya ya kasance na gaskiya wanda ya ginu bisa adalci, 'yanci da kafa kasa mai cin gashin kanta ga al'ummar Palastinu.

Trump Ya yi iƙirarin cewa: Idan ya yi nasara a zaben shugaban kasar Amurka, zai kawo karshen yake-yake da zubar da jini, musamman a Gaza da Ukraine, domin kuwa a cewarsa shi dan takarar zaman lafiya ne.

 

 

4246887

 

 

captcha