Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Al-Masri Al-Youm ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Masri Al-Youm cewa, a daren jiya da dare ne Osama Al-Azhari, ministan kula da harkokin addini na kasar Masar ya bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 31 a kasar Masar.
Wannan gasa wadda aka fara a ranar Asabar 7 ga watan Disamba a karkashin kulawar ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar, ta kare ne a ranar 20 ga watan Disamba tare da rufe gasar da kuma bayyana sakamakon bayan sallar magriba a masallacin da cibiyar al'adu ta Masar a sabon tsarin gudanarwa babban birnin kasar.