Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Awsat cewa, ofishin yada labarai na karamar hukumar Sirte ya sanar da cewa, a wannan aiki, an kwace kur’ani masu karamin karfi a aljihu guda 1,610, sakamakon samun wasu kalmomi da ba a iya gane su ba kamar sihiri.
Shugaban jami'an tsaro reshen Sirte ya bayyana cewa: A cikin wata wasika da ma'aikatar kula da waqaqa ta Libiya ta aikewa da su ta bukaci a tattara wadannan kur'ani da aka yi amfani da su a matsayin kayan ado a cikin motoci.
Ya kara da cewa: Wadannan kur’ani masu dauke da kalmomi marasa fahimta kamar sihiri da sunayen shaidanu, an mika su ga ofishin bayar da tallafi na Sirte bayan an tattara su.