An gudanar da wannan biki ne a cikin tsarin kiran da kungiyar Musulunci ta yi na gudanar da jana'izar Sayyid Hassan Nasrallah a yankuna daban-daban na kasar Bahrain tare da taken "Muna da tsayin daka kan alkawarinmu."
Mahalarta bikin sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da adawa da daidaita alakar kasarsu da gwamnatin yahudawan sahyoniya, tare da nuna adawa da duk wani kasancewar sahyoniyawan a kasar Bahrain.
A jiya 21 ga watan Febrairu ne aka gudanar da bikin jana'izar gawawwakin wadannan shahidai guda biyu masu tsarki tare da halartar jama'a da dama a lardunan Dhi Qar da Nasiriyyah na kasar Iraki. Wannan biki ya nuna zurfin sadaukarwa da girmamawar al'ummar Iraki ga shahidan Sayyid Hassan Nasrallah da Sayyid Hashem Safi al-Din.