IQNA

Gwamnatin Burtaniya ta damu da karuwar kyamar Musulunci

16:19 - April 11, 2025
Lambar Labari: 3493077
IQNA - Yunkurin nuna kyama ga musulmi a Burtaniya ya haifar da damuwa a tsakanin gwamnatin Labour.

A cewar Aljazeera, ga dukkan alamu jam'iyyar Labour ta Burtaniya na kara fuskantar barazana daga kalaman kyamar musulmi a kasar, inda alkaluma ke nuna yadda ba a taba samun irin wannan tsattsauran ra'ayi kan al'ummar musulmi ba. Jawabin populist na hannun dama ya shahara musamman akan layi.

Yayin da ake kara nuna fargabar cewa gwamnati ba ta daukar kyamar Musulunci da muhimmanci, Ministan harkokin addini Wajid Khan, ya sanar da cewa za a ware kusan fam miliyan 1 (£1.29) don kafa wata kungiya mai zaman kanta da za ta sanya ido tare da bayar da rahoton laifukan kyama ga musulmi da kuma tallafawa wadanda abin ya shafa.

Matakin na gwamnatin ya biyo bayan alkalumman da wasu majiyoyi da dama suka fitar, musamman ‘yan sandan Birtaniya, sun yi gargadin karuwar korafe-korafen kalaman kyama da wariyar launin fata ga musulmi da ba a taba yin irinsa ba; ‘Yan sanda sun bayyana karuwar al’amuran kyamar Musulunci da kashi 73 cikin 100 a bara, inda kashi 40% na tashe-tashen hankula a shekarar 2024 ke da nasaba da addini da ya shafi musulmi.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Birtaniya Tell Mama da ke aikin yaki da kalaman kyamar musulmi, ta ce ta samu mafi yawan korafe-korafe na kalaman nuna kyama ga musulmi a kasar a cikin shekarar da ta gabata, mafi girma tun bayan kafa kungiyar shekaru 12 da suka gabata.

Dangane da wani hoto mai cike da damuwa da gwamnati da hukumomi masu zaman kansu suka zana na saurin yaduwar kyamar Musulunci a Burtaniya, gwamnatin kasar ta yi tafiyar hawainiya wajen samar da dokokin hukunta masu aikata laifuka.

A cikin makonnin da suka gabata, gwamnatin Labour ta kafa wani kwamitin ba da shawara na kwararru don samar da ma'anar kyamar Musulunci da kuma taimakawa hukumomin gwamnati da 'yan sanda wajen shawo kan korafe-korafen kyamar Musulunci da kalaman kyama ga musulmi.

A lokacin yakin neman zabe, jam'iyyar ta yi alkawarin daukar wani ma'anar kyamar Musulunci da kungiyar 'yan majalisar dokoki ta All-Party (APPG) ta tsara a 2019, wanda zai ayyana ayyukan da ake yi wa Musulunci da Musulmai a matsayin wariyar launin fata, idan ta hau mulki.

 

4275777

 

 

captcha