A cewar Rai Al-Youm, Mahmoud Al-Qawud ya rubuta wasika zuwa ga Mohamed Shawqi Ayyad, babban lauyan kasar Masar, inda ya bukaci ya gurfanar da Ibrahim Issa a gaban kuliya bisa zargin cin mutuncin addinin Musulunci, tozarta kur’ani, da kuma bata fuskar Manzon Allah (SAW).
Wasikar ta bayyana cewa, Ibrahim Issa, dan jarida kuma ma'aikacin cibiyar sadarwar tauraron dan adam ta Al-Hurra ta Amurka, ya aikata ayyukan ta'addanci karara a cikin shirye-shiryensa na wannan kafar sadarwa na cin mutuncin addinin Musulunci bayyananne, da wulakanta kur'ani, da kuma cin mutuncin matsayin manzon Allah (SAW) da gangan.
A daya daga cikin wadannan shirye-shiryen ya yi inkarin ma'asumi na Manzon Allah (SAW) da tsantsar dabi'arsa, yana mai cewa Manzon Allah (SAW) yana shan giya. Yayin da wannan lamari ya ci karo da kimar Musulunci gaba daya, kuma yana haifar da rashin gamsuwa a tsakanin musulmi.
Har ila yau Ibrahim Issa ya bayyana a cikin wani shiri mai taken "Alkur'ani; "Zaluntar mata" tare da tsokaci masu tayar da hankali da kuma haifar da shakku, ya yi da'awar cewa kur'ani na kunshe da abubuwa da suka shafi zalunci da ake yi wa mata, wanda ke nuni da kai hari ga tsarkakar kalmar Allah da kokarin haifar da damuwa a tsakanin musulmi dangane da matsayin kur'ani mai tsarki.
Nassin wasikar ya kuma yi nuni da cewa, ta hanyar karbar malaman da ba su da alaka da addini, da kuma samar da damammaki na cin mutuncinsu, ya ba da dama ga daidaikun mutanen da a fili suke nuna rashin yarda da Allah su rika cin mutuncin zatin Allah mai tsarki da kuma darajar Manzon Allah (SAW), wanda hakan ya kai matsayin yunkurin tayar da kiyayya da fitinar addini.