Kamfanin dillancin Ikna ya nakalto daga jaridar Almadina ta kasar saudiyya cewa; za a gudanar da wani taron girmama 'yan mata mahardata kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya wanda diyar sarkin Saudiyya za ta jagoranci mika kyaututtuka. Cibiyar kula da gasar Kkur'ani ta kasar Saudiyya ce ta shirya gudanar da taron, inda 'yan mata da suka hardace kur'ani daga sassa daban-daban na kasar za su samu halartar taron, kuma za su karbi kyaututtuka daga diyar sarki Saudiyya . Bangaren kula hulda da jama'a na cibiyar ya sanar cewa babbar manufar gudanar da taron dai ita ce karfafa gwiwar 'yan mata da suka hardace kur'ani wajen bayar da himma, kamar yadda hakan zai karfafa gwiwar wadanda ba su samu sun hardace ba.
392883