Bangaren kasa da kasa: masana da kuma manazarta musulmi a nahiyar turai sun gudanar da wani zama a yau a birnin Amstardam na kasar Holland, domin yin dubi dangane da matsalolin da musulmi suke fuskanta a kasashe daban-daban da ke nahiyar turai, musamman ma dai matasa daga cikinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na radio Holland cewa; masana da kuma manazarta musulmi a nahiyar turai sun gudanar da wani zama a yau a birnin Amstardam na kasar Holland, domin yin dubi dangane da matsalolin da musulmi suke fuskanta a kasashe daban-daban da ke nahiyar turai, musamman ma dai matasa daga cikinsu. Daga cikin abin da zaman ya fi mayar da hankali a kansa akwai batun yada munan bayanai kan addinin musulunci da kafofin yada labarai na kasashen turai ke yi, daga ciki kuwa har da ma kafofin yada labarai mallakin gwamnatoci, mahalarta taron sun jaddada wajabcin tunasar da gwamnatocin turai irin hadarin da ke tattare da yin hakan.
405631