IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Ta Soki Lamirin Isra'ila

16:07 - August 06, 2009
Lambar Labari: 1810241
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta soki lamirin haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da yadda take ci gaba da yin fatali da shirin wanzar da zaman lafiya tsakaninta da palastinawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran kasar Kuwait cewa; Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta soki lamirin haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da yadda take ci gaba da yin fatali da shirin wanzar da zaman lafiya tsakaninta da palastinawa, da kuma yadda Isra'ila take ta hankoron mayar da birnin Qods na yahudawa zalla. Masu gudanar da zanga-zangar sun daga tutocin kungiyoyin gwagwarmaya na Hamas da hizbullah, da hotunan wasu daga cikin wadanda suka yi shahada a hare-haren ta'addancin da sojojin Isra'ola suka kai akn al'ummomin labanan da palastinu. Sun gudanar da zanga-zangar ne a gaban ofishin jakadancin kasar Azarbaijan da ke birnin Istanbul.
443363
captcha