IQNA

Makaranta 11 Sun Kara Da Juna A Gasar Kur'ani Ta Kasar Malazia

21:17 - August 08, 2009
Lambar Labari: 1810864
Bangaren kasa da kasa; Makaranta goma sha daya ne suka kara da juna a dare na uku a gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar malazia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Makaranta goma sha daya ne suka kara da juna a dare na uku a gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar malazia.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani ta sarki fahad ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan taro, inda aka fitar da wasu daga cikin muhimman kayan tarihi da ke bayyana fasahar addinin musulunci tun tsawon shekaru sama da dubu daya da suka gabata. Taron yana samun halartar masana dake gudanar da bincike kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi tarihin musulunci, daga cikin kasar da ma wajen kasar.
444415



captcha