IQNA

Sudan Za Ta Dauki Bakuncin Taron Cinikayyar Kasashen Musulmi

10:39 - October 03, 2009
Lambar Labari: 1832620
Bangaren kasa da kasa; Sudan za ta dauki nauyin bakuncin taron jami'an harkokin kudade da cinikayya na kasashen musulmi, wanda za a gudanar a karo na shida a makon gobe a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Sudan za ta dauki nauyin bakuncin taron jami'an harkokin kudade da cinikayya na kasashen musulmi, wanda za a gudanar a karo na shida a makon gobe a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka gwamnatin Sudan din ta kallama dukkanin shrye-shiryen da suka kamata domin karbar bakuncin wannan zaman taro, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi. 472699



captcha