Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna net a watsa rahoton cewa: a taron kasar Girka da aka gudanar an tabo batun yadda za a tabbatar da sulhu da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya musamman hanyoyin da ke hana ruwa gudu a duk wani kokari na magance matsalar rikici da tashin hankali da zai kai ga tabbatar da zaman lafiya a yankin.Sai dai ko ba komi matsalar da halin da Palasdinawa ke ciki na mamaye da zalumcin haramtacciyar kasar Isra'ila shi ne ya mamaye wannan taro ko ba a sani ba ko mahalarta taron za su iya yin wani habbasa kan wannan matsala har su kai ga cimma nasara da burin gudanar da wannan taro ko a'a lokaci ne kawai zai amsa mana wannan tambaya.
477296