Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na naharnet cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Labanan ya bukaci da a kawo karshen killace yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya ke yi wa fararen hula a yankin.Bayanin ya ci gaba da cewa kakakin majalisar dokokin kasar ta Labanan Nabih Birri, ya kira ne ga dukkanin gwamnatocin da suke da hakkin daka wa Isra'ila birki kan tabargazar da take tafkawa a duniya, wanda acewarsa hakan ya saba wa dokoki na kasa da kasa. 595604