IQNA

Bude Sansanin Koyar Da Ilmin Addini Ga Sabbin Musulunta A Holland

15:24 - July 03, 2010
Lambar Labari: 1950102
Bangaren kasa da kasa; An bude wani sansanin koyar da ilmomin addinin Musulunci da wayar da kai ga wasu da suka karbi addinin a kasar Holland, wanda cibiyar musulmin kasar ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an bayyana cewa, yanzu haka an bude wani sansanin koyar da ilmomin addinin Musulunci da wayar da kai ga wasu da suka karbi addinin a kasar Holland, wanda cibiyar musulmin kasar ta shirya. Bayanin ya ci gaba da cewa a wannan sansani ana koyar da mutanen ilmomi na akida da kuma shari'a, gami da wayar da kansu kan koyarwar Musulunci dangane da sauran harkoki na rayuwar zamantakewa. 607760



captcha