Kamfanin dillancin labaan iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na Muhit an habarta cewa, ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci a kasar Masar Mahmud Hamdi Zaqzuq ya sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar hardar kur'ani mai tsarki ta masu tabin hankali a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa ministan ya fitar da sunayen mutane shida ne da suka lashe gasar, kuma za a gudanar da taro na musamman domin girmama su tare da ba su kyautuka na musamman.
Wannan gasar takan hada mutane ne daban-daban da suke da matsalar kwakwalwa a kasar ta masar, inda a kan ba su dama su gudanar da hardar kur'ani mai tsarki.
639514