Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da ake dubar watan shawal a birnin Najaf Ashraf da ke kasar Iraki, an watan ne daga kan rufin makarantar babban malamin nan malam Akhund da ke cikin birnin mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun bayan da aka bada sanawar a duba wata a birnin daga babbar cibiyar addinin Musulunci da mabiya tafarkin iyalan gidan manzo na kasar suke komawa zuwa gare ta, al'umma suka fantsama waajen dubar wata.
Daga cikin mutanen da suke hawa kan shigihu domin dubar wata, wasu daga kan rufin makarantar babban malamin sun tabbatar da ganinsa.
652053