Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran na yanar gizo cewa, Jagoran juyin juya halain Musulunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa samun hadin kai tsakanin al'ummar musulmi shi ne kadai hanyar kalubalantar makiyan Musulunci.
A cikin hudubar sallar idi na karamar sallah da ya gabatar jiya a masalacin Juma'a na birnin Tehran inda aka gabatar da sallar idi, jagoran ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin al'ummar musulmi baki daya, ta yadda za su iya gudanar da lamurransu yaka junansu.
Ya ce bisa la'akari da irin barazanar da musulim da kuma addinin muslunci ke fuskanta, su musulmin ne za su iya taka wa cin zarafi da tozarci birki ta hanyar hada kansu, domin kuwa duk wata rarraba a tsakaninsu kuskure ne mai girma.
652155