Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar kasar masar ta Yau Sabi cewa, Babban malamin jami'ar Azhar ta masar ya bayyana cewa abin da ya faru na kone wasu masu kiran kansu kirista suka a kasar Amurka a ranar tunawa da hare-haren 11 ga watan satumba babban wawanci ne, kuma ba addinin kiristanci ba ne.
Malamin ya ci gaba da cewa wadanda suka yi wannan wawanci suna zaton za su iya cutar da littafin Allah madaukakakin sarki, to su kwana da sanin cewa babu abin da zai samu wanan littafi mai tsarki.
Ya kara da cewa masu irin wannan mummunan tunani dukkansu 'yan tsiraru ne, domin kuwa al'ummar Amurka da dama sun fito sun nuna goyon bayansu ga musulmi.
653376