Bangaren kasa da kasa; Da dama daga cikin malaman addini da kuma marubuta akasar Libya sun bayyana cewa, babbar manufar mutumin da ke kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki a Amurka ba wani abu ba ne illa neman suna kawai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar kasar Masar cewa, da dama daga cikin malaman addini da kuma marubuta akasar Libya sun bayyana cewa, babbar manufar mutumin da ke kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki a Amurka ba wani abu ba ne illa neman suna kawai a duniya da kuma tsakanin al'ummar kasar.
Masanan sun yi imanin cewa mutumin da ke kallon kansa a matsayin malamin addinin kirista, kuma majami'ar da yake tara mutane tana gab da tarwatsewa saboda ba shi da abin da zai gaya ma masu taruwa, shi ne ya kirkiri kira zuwa ga kone kur'ani mai tsarki domin ya sama kansa suna.
653528