Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na nun an bayyana cewa, jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Iraki Hassan Danai far ya kai wata ziyara ta musamman a birnin Karbala mai alfarma, inda ya gana da manyan jami'ai na birnin mai alfarma.
Bayan ziyara da ya kai a wurare masu tsarki dake birnin, jakadan Iran ya gana da Sheikh Abdulmahdi Karbala'i da ke kula da hubbaren Imam Hussain (AS), kuma wakilin Ayatollah Sistani a Karbala.
Bayanin ya ci gaba da cewa birnin Karbala mai alfarma yana samun ci gaba cikin sauri, sakamakon yawan maziyarta daga sassa-daban na duniya da ke ziyartar birnin mai albarka.
658789