Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kuna cewa, za a gudanar da wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta mata a kasar Kuwait wadda ma'aikatar kula da harkokin addinin msulunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a cikin makon nan da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka dai babbar cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani ta kasar ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da wannan gasa, da za ta samu halartar makanta da kuma mahardata daga sassan kasar.
Babban jami'in da ke kula da shirya gasar a mataki na kasa ya bayyana cewa bayan kammala gasa za a bayar da kyautuka na musamamn ga dukkanin wadanda suka nuna kwazo.
659547