Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, bankin duniya ya amince da majlisar rikon kwarya ta kasar Libya a matsayin mai wakiltar kasar a hukumance a cikin dukaknin lamurran al'ummar kasar ta Libya, da nufin sake farfado alaka tsakanin bangarorin biyu.
A karon farko tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi a kasar Libiya shugaban Majalisar Wucin Gadi da ke wakiltan masu bore a kasar Mustafa Abdul-Jalil ya shiga birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta Libiya a jiya asabar.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Libiya a Majalisar Wucin Gadin kasar Ahmad Dharad ya bayyana cewar zuwan Mustafa Abdul-Jalil cikin birnin Tripoli dalili ne da ke tabbatar da cewar mulkin kama karya na Mu'ammar Gaddafi ya kawo karshe a kasar Libiya.
Daruruwan jama'a ne suka tarbi shugaban Majalisar Wucin Gadin Mustafa Abdul-Jalil bayan isarsa birnin na Tripoli karkashin tsauraran matakan tsaro.
860838