Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na echoroukonline an bayyana cewa, a wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Alkahira, fitaccen dan siyasa kuma tsohon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Muhammad Albaradei ya buakci majalisar sojin kasar masar da ta saka tsari na mayar mulkin kasar ga hannun farar hula a cikin kankanin lokaci, bisa la’akari da yadda ake ta samun matsaloli a kasar.
Ya ce rashin sanin takamai inda aka nufa akasar shi ne babban abin da ya jefa mutane cikin wani yanayi na zullumi da rashin tabbas, amma idan aka samu hanyar da za a mayar da mulkin ga hannun farar hula ta hanyar lumana, su kansu sojoji za su huta da tsangwamar jama’ar kasar.
Yanzu haka dai tsohon shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Muhammad Albaradei ya buakci majalisar sojin ta kasar masar da ta saka tsari na mayar mulkin kasar ga hannun farar hula, da hakan zai hada da ‘yan siyasa da kuma matasa da suka yi juyin juya hali.
881568