Bangaren kasa da kasa:hukumar da ke kula da kare hakkokinnbil adama ta larabawa a Britaniya AOHR a ranar shidda ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ta fitar da wani bayani a daidai wannan rana ta duniya ta yaki da azabtarwa da cewa haramtacciyar kasar Isra'ila it ace daya –dayar gwamnati a cikin jerin gwamnatocin duniya da ta amince da amfani da azabtarwa da tursasawa fararen hula domin cimma bakaken manufofinta.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; hukumar da ke kula da kare hakkokinnbil adama ta larabawa a Britaniya AOHR a ranar shidda ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ta fitar da wani bayani a daidai wannan rana ta duniya ta yaki da azabtarwa da cewa haramtacciyar kasar Isra'ila it ace daya –dayar gwamnati a cikin jerin gwamnatocin duniya da ta amince da amfani da azabtarwa da tursasawa fararen hula domin cimma bakaken manufofinta.Majiyar labarai ta Palestine Info ta watsa rahoton cewa: wannan hukumar ta kare hakkin dan adam a cikin bayanin da ta fitar ta bayyana cewa: azabtarwa da tursasawa tabka babban leifi ne ko wane iri ne kuma take hakkin dan adam ne karara. Kuma sun yi kira da gwamnatoci da kasashen duniya das u hukumta wannan matsala ta azabtar dawani farar hula ba tare da sun yi la'akari da ina ne aka aikata hakan kuma kan wane ne aka aikata wannan leifi na azabtar da wani farar hula kuma dan adam abin girmamawa da kare masa hakkinsa.
1039430