IQNA

Hana Maniyyata Daga Kasashen Syria Da Yemen Zuwa Hajji Da Al-Saud Suka Yi Babban laifi Ne

23:27 - September 20, 2015
Lambar Labari: 3365561
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Abdussattar Sayyid minister mai kula da harkokin addi a kasar Syria ya bayyana hana alhazan Syria da na Yemen zuwa hajjin bana da mahukuntan Saudiyya Suka yi da cewa babban laifi ne maras misiltuwa.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran SANA na kasar Syria cewa, Muhammad Abdussattar Sayyid a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a wajen taron girmama wasu mahardata kur’ani 100 jiya a garon Tartus, ya ya bayyana hana alhazan Syria da na Yemen zuwa hajjin bana da mahukuntan Saudiyya Suka yi da cewa babban laifi ne mai girma.

Ya ce ci gaba da gudanar da ayyuka da suka shafi kur’ani mai tsarki lamari ne da ke tabbatar da cewa addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai kamar yadda ya koyar, ba kafirta musulmi da ta’addanci ba kamar yadda wasu suke son su nuna cewa hakan shi ne musulunci.

Ma’aikatar kula da ayyukan addini a lardin Tartus ta dauki nauyin shirya gdanar da wanan taro ne da nfin girmama wadannan dalibai 100 da suka nuna kwazo matuka wajen hardar kur’ani mai tsarki, kuma wannan ya nuna yadda ake mayar da haknali ga lamarin kur’ani da koyarwarsa  akasar duk da matsalolin da aka haddasa a cikinta.

A taron an nuna yadda ake koyar da kur’ani mai tsarki ga kananan yara a cikin harsunan larabci da kuma faransanci, wanda hakan ya kara karfafa wannan lamari na koyar da kur’ani mai tsarki musamman  ama tsakanin yara da matasa.

Gwamnonin lardin Tartus da Hama duk sun halarci taron, wanda cibiyar Assad ta shirya, wanda kuma akwai rassa wannan cibiya 13 a yankin.

3365249

Abubuwan Da Ya Shafa: syria
captcha