Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, an gudanar da wanann taro ne a jiya wanda ya yi daidai da ranar 18 ga watan Zilhijjah, ranar da ta zama muhimmiyar rana ta tarihin muslunci da cikar ni’imar ubangiji ga talikai.
Wannan rana na daya daga cikin ranaku da mau imani suke gudanar da taruka na farin ciki a koina domin tunawa da kuma raya wanann rana da Allah ya cika haskensa da ni’arsa ga bayinsa.
A kan haka ne dubban masu imani suka hadu a wannan hubbare mai tsarki na Sayyidah Zainab a kusa da birnin Damascus na kasar Syria suka gudanar da wannan taro mai tarin albarka, tare da jadda wajabcin ci gaba da bayyana matsayin wannan rana da kuma raya ta, domin yin hakan shi ne raya hakikanin addinin Allah da anzonsa.
Sheikh Muhammad Ibrahim Khalil, shugaban karamin ofishin kasar Iran na ala’du a kasar Syria ya bayyana a wajen taron cewa, wannan taro yana da matukar muhimamnci ga dukaknin al’ummar musulmi, kuma za a ci gaba da yin hakan da yardarm domin samun albarkacin wannan rana.
Baya ga tawagar mutanne Syria da kuma iraniyawa, an samu halartar mutane da dama daga kasashen larabawa a wajen wanann taro mai albarka.
3377462