IQNA

Shin Za A Kwace Hakkin Zama Dan Kasa Daga Dan Sheikh Nimr?

16:19 - January 18, 2016
Lambar Labari: 3480052
Bangaren kasa da kasa, furucin da Muhammad Nimr ya yi kan iyalan Saud ya sanya hakan ya jawo fushinsu tare da yin kira da akwace hakkinsa na zama dan kasa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tayyar.org cewa, Muhammad Nimr da ga sheikh Nimr Bakir Nimr fitaccen malamin addinin mulunci a kasar Saudiyyah da mahukuntan kasar suka kashe, ya yi furucin da ya jawo fushin mahukuntan kasar.

A lokacin da yake zantawa da wata tashar talabijin ta kasar Amurka NPR ya bayyana cewa; yana alfahari da abin da mahaifinsa ya aikata, domin kuwa babbar manufarsu ita ce sanar da al’ummar duniya halin zalunci da danniyar da ake yi kansu, amma duniya ba ta saurarensu, abin da mahaifinsa ya yi, ya tabbatarwa duniya gaskiyar cewa Al Saud azzalumai ne.

Wannan furuci na Muhammad Nimr da ya yi ta yada shi a kafofi na sadarwa na yanar gizo, inda wasu masu goyon bayan gidan sarautar zalunci suke yin kira da a kwace hakkinsa na zama dan kasa kuma a kore shi ko kuma dauki mataki a kansa.

3468163

captcha