
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Star cewa, Haruna Musa, Ramadan Sabwa, Ramadan Nadja, Isma’ila Wureh, da Yusuf Malala su ne mutane 5 da suka shirya domin gudanar da tarjamar kur’ani mai tsarki.
Haruna Musa shi ne wanda ya kirkiro shirin bayan da ya fito daga gidan kaso da aka kame shia cikin shekara ta 2014, bisa zarginsa da kasancewa mamba nay an ta’addan Al-shabab.
Musa ya ce ya fahimci cewa ya zama wajibi a gudanar da irin wannan aiki na addini, domin kuwa zai zama babban taimako ga mutanen da bas u jin larabcia yankin yammacin Kenya ta hanyar tarjama kur’ani da harshensu.
Ya kara da cewa idan suka gudanar da wannan aiki na tarjama kur’ania cikin harshen Luhiya, to zai zama aiki irinsa na farko da aka gudanar mai matukar muhimamnci.
An gudanar da taron fara wannan aiki a babban masallacin mamyas da ke yammacin kasar ta Kenya, tare da halartar musulmi da dama, wadanda suka nuna matukar gamsuwarsu da hakan, tare da bayar da dukaknin goyon baya ga wadanda suka kudiri aniyar aiwatar da wannan aiki.