IQNA

Musulmi Mata Masu Lullubi Suna Fuskantar Matsaloli A Ingila

23:21 - August 12, 2016
Lambar Labari: 3480703
Bangaren kasa da kasa, wani rahoto da kwamitin kare hakkokin mata da daidaito a tsakanin al’umma na majalisar dokokin Birtaniya ya nuna damuwa kan wariyar da ake nuna ma mata musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewam ya nakalto daga tashar talabijin ta Press TV cewa, jaridar Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, kwamitin kare hakkokin mata da daidaito a tsakanin al’umma na majalisar dokokin Birtaniya ya fitar da sakamakon bincikensa kan halin da mata musulmis uke ciki a kasar.

Rahoton ya ce mata musulmi masu sanye da hijabi su ne suka fi fuskantar matsala wajen aikin yi akasar, idan aka kwatanta da mata wadanda ba musulmi ba, wanda hakan lamari mai matukar hadari.

Haka nan kuma rahoton ya yi nuni da yadda wasu mata musulmi sukan fuskanci matsin lamaba a wuraren da suke yin aiki, ta yadda ala tilas sukan cire lullubin da ke kansu matukar dai suna son su ci gaba da yin aiki domin smun abin da za su ciyar ‘ya’yansu da daukar nauyin karatunsu.

Kwamitin ya ce abin da mata musulmi suke fuskanta na takuwara da gallazawa a kasar ta Birtaniya ya yi hannun riga da dokokin kasar, kuma yin hakan take hkkokin bil adama, wanda ya kamata a dauki mataki a kansa.

Yanzu haka dai akwai mata musulmi da dama wadanda ‘yan kasar Birtaniya, amma ba su da aikin yi, saboda kin daukarsu aiki a kamfanoni ko ma’aikatun gwamnati, saboda saka hijabin muslunci da suke yi.

3522052

captcha