Daga cikin kungiyoyin da suka mayar da martini kuwa har da Jabha, inda ta fitar da bayani da ke cewa, babban abin kunya e kasa kama Saudiyya wadda ke aiki kafada da kafada tare da makiya adinin muslunci wajen rusa kasashen larabawa da na muuslmi a yankin gabas ta tsakiya da Sauransu, har ta iya ta fitar da wata al’umma guda daga addinin muslunci.
Bayanin kuniya ya ce hakan abin yin Allawadai ne da kakkausar murya, tare da kiran masarautar iyalan gidan da Saud da ta sanya wannan mutum fitar da wannan mummunar fatawa ta siyasa da ta gaggauta tilasta ya jane fatawar, domin samun zaman lafiya atsakanin al’ummar musulmi.
A cikin wannan makon ne babban mai bayar da fatawa ga ‘ya’yan Saud ya fitar da fatawar kafirta dukkanin al’ummar Iran, bisa hujjar cewa su jikokin majusawa ne masu bautar wuta.
Wasu daga cikin masana daga sassa na duniya da na ci gaba da yin Allah wadai da wannan mummunan furuci, yayin da wasu suke bayyana shi mai fatawar da masarautar da ta sanya a matsain cewa bisa dogaro da hujjar da ya bayar wajen kafirta Iraniyawa su ma za su iya zama a matsayin hakan, domin kuwa su ma jikokin mushrikai ne mas bautar lata da uzza.
Masaurautar yayan Saud ta kidime ne sakamakon saon da jagoran juyin juya halin muslunci ya aike wa alhazai, da ke kiransu da su zama masu ‘yanci a cikin lamarinsu an addini, da kuma ‘yantar da wurare masu tsarki su zama karkashin kulawar al’ummar musulmi baki daya, domin kaucewa abin da ya faru na kisan dubban bayin Allah a shekaar da ta gabata alokacin da suke aikin hajji.