IQNA

Taron Kasa Da Kasa A Algeria Kan sahihiyar Fahimtar Kur'ani

22:24 - December 04, 2016
Lambar Labari: 3481003
Bangaren kasa da kasa, yau ne aka bude taron kasa da kasa na shekara-shekara kan sahihiyar fahimtar kur'ani a karo na shida, wanda yake gudana a jami'ar Musulunci ta birnin Kusantina a kasar Algeria.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya bayar da rahoton cewa, a yayin bude zaman taron, Muhammad Isa minista mai kula da harkokin addini a kasar Algeria ya bayyana cewa, fahimtar kur'ani mai tsarki sahihiyar fahimta, ita ce mabudin dukkanin ci gaba a rayuwar musulmi a duniya, kuma hanyar tsirarsa a lahira.

Muhammad Isa ya kara da cewa, bisa la'akari da muhimmancin da ke tatatre da yada fahimtar kur'ani a tsakanin musulmi sahihiyar fahimta, hakan yasa aka fara gudanar da wannan shiri tun tsawon shekaru shida, domin kuwa ta hanyar wayar da kan musulmi ne za a kaucewa fadawa kan tafarkin karkatacciyar fahimta kan muslunci, wanda kuma hakan ne kan kai matasa ga ayyukan ta'addanci.

Taron yana samuhn halartar malamai da masana daga cikin kasar ta Algeriya da kuma kasashen duniya daban-daban, musamman na muuslmi da larabawa.

3550709

captcha