IQNA

UNICEF: Za Mu Gudanar Da Bincike Kan Cin Zarafin Yara Musulmi A Myanmar

22:52 - February 06, 2017
Lambar Labari: 3481206
Bangaren kasa da kasa, asusun tallafa wa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF na shirin gudanar da bincike kan cin zarafin kananan yara 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, Hukumar ta UNICEF ta sanar da hakan ne jiya, kwanaki biyu bayan fitar da rahoton kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, wanda ya tabbatar da cewa jami'an tsaron gwamnatin Myanmar tare da masu tsatsaurean ra'ayi daga cikin mabiya addinin buda sun tafka laifukan yaki a kan musulmi 'yan kabilar Rohingya.

Rahoton na kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi ishara da cewa, jami'an tsaron na Myanmar da 'yan addinin buda sun kashe musulmi masu tarin yawa, da suka hada da mata da kuma kananan yara da tsoffi, haka nan kuma sun yi ma mata da dama fyade, kamar kuma suka rusa musu gidaje tare da kone kaddarorinsu.

Bisa dogaro da wannan rahoto, hukumar UNICEF ta ce za ta gudanar da bincike musamman kan kanan yara da wannan lamari ya rutsa da su, kuma za ta bukaci da a dauki mataki na shari'a a kan dukkanin wadanda suke da hannu wajen muzgunawa ko cin zarafin kananan yara 'yan kabilar Rohingya akasar ta Myanmar.

3570785


captcha