Wadanda suka sheda lamarin sun ce jami'an sojin gwamnatin Myanmar sun kai farmaki a ranar Juma'a ashirin da biyar ga ga watan Agustan da ya gabata a kauyen chut pyn dake cikin yankinRathedaung, inda suka kashe daruruwan mata da kananan yara, ta hanyar jefa su a cikin wuta suna kona su.
Haka nan kuma sukan yi amfani da manyan adduna wajen sare kawunan duk wani musulmi da suka gani a yankin, sun kona dukkanin gidajen musulmi da ke yankin baki daya, tare da dukkanin kaddarorinsu.
A nasa bangaren shugaban kungiyar musulmi 'yan kabilar Rohingya mazauna nahiyar turai Anita Shug ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran anatoli a jiya cewa, bisa rahotannin da suk tattara dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a kasar Myanmar, an rusa tare da kone dubban gidajen musulmi tare da kashe fiye da dubu biyu a cikin kimanin mako guda da ya gabata.
Wannan a cikin gundumar rakhin ne kawai, yayin wasu fiye da dubu dari kuma suka tsere suka bar yankunansu domin tsira da rayuwarsu, ba tare da sanin inda za su nufa ba, wanda hakan yasa wasu daga cikin su suke mutuwa a hanya, sakamakon raunuka da suka samu, ko kuma yunwa da rashin abicnin da za su ci.
Baya ga haka kuma wasu suna mutuwa a cikin koramu a lokacin da suke tsallakawa domin tsira daga hare-haren sojojin gwamnatin Myanmar, musamman mata da kananan yara.