IQNA

Za Ma A Birnin New York Kan Matsalar Rohingya A Myanmar

17:08 - September 06, 2017
Lambar Labari: 3481871
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya bayyana cewa za a gudanar da wani zaman a kasa da kasa kan batun matsalar da musulmin Rohingya a birnin new York.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na dailysabah cewa, Maulud Jawish Auglo ministan harkokin wajen Turkiya ya bayyana cewa, za a gudanar da zaman a kasa da kasa a gefen zaman babban taron majalisar dinkin duniya a birnin New York.

Y ace aron zai samu halaratr babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres tare da wasu daga cikin shugabannin kasashen duniya da suke nuna goyon bayansu da damuwarsu kan halin da musulmi 'yan kabilar Rohinya suke ciki a kasar Myanmar.

A ranar Juma'a da ta gabata ce rundunar sojin kasar Myanmar ta sanar da cewa, daga ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata mutane 370 kawai suka kasha daga cikin msuulmi 'yan kabilar Rohingya.

Amma majalisar musulmi 'yan kabilar Rohingya mazauna nahiyar turai ta tabbatar da cewa,a cikin wannan mako an kasha musulmi 2300 a cikin kwanakin uku kawai.

Yanzu haka dai akwai fiye da musulmi dubu dari da talatin da suka tsallaka zuwa kasar Bangaladesh domin tsira da rayukansu, yayin da wasu suka mutu a hanya, wasu kuma suka lakahe a cikin koramu.

3639084


captcha