IQNA

Muhammad Na Daga Cikin Sunayen Da Suke Yaduwa A Austria

23:39 - January 07, 2018
Lambar Labari: 3482276
Bangaren kasa da kasa, wani bincike ya nuna cewa sunan Muhammad shi ne na uku a cikin sunayen da uka fi yaduwa a cikin Austria a cikin shekara ta 2017.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saumaria News cewa, jaridar Croning Zetong ta kasar Austria ta ayar da rahoton cewa, bisa wani bincike da ta gudanar ta gano Muhammad shi ne suna na uku da yafi yaduwa a kasar a shekarar da ta ta gabata.

Rahoton ya ce wasu suna saka Muhammad, wasu kuma Muhamed, wasu Muhamad, amma duk da haka sunan ya zo na uku.

Sunayen da suk na farko da na biyu a kasar Ausria a shekarar da ta shude su ne Alexender sai kuma Maksimilian, sai kuma Muhammad a matsayi na uku.

A kasar Birtaniya ma an bayyana cewa  ahalin yanzu sunan Muhammad yan da cikin sunae 10 da suka fi yaduwa  akasar.

Kasar Austria ta karbi ‘yan gudun hijira musulmi kimanin dubu 90 a cikin 2015, wanda suke a matsayin kashi daya na mutane miliyan 8 da suke rayuwa  a kasar.

3679717

 

 

 

 

 

captcha