IQNA

Yin Bayani Kan Musulunci Ga Wadanda Ba Musulmi Ba A Madrid

23:13 - February 06, 2018
Lambar Labari: 3482371
Bangaren kasa da kasa, mabiya adinin muslunci mazauna birnin birnin Madrid na kasar Spain za su gudanar da shirin bude kofofin masallatai ga wadanda ba musulmi ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sadal balad cewa, mabiya adinin muslunci mazauna birnin birnin Madrid na kasar Spain za su gudanar da shirin bude kofofin masallatai ga wadanda ba musulmi ba a birnin.

Mabiya addinin musulunci a wasu daga cikin kasashen turai suna yin haka a kowace shekara, inda sukan gayyaci wadanda ba musulmi ba zuwa masallatansu da cibiyoyinsu domin ganin yadda musulmi suke gudanar da harkokinsu.

Babbar manufar hakan dai ita ce kara samar da yanayi na fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran mabiya wasu addinai.

Babbar cibiyar musulmi mazauna birnin na Madrid ce za ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri tare da hadin gwiwa da cibiyar Azhar.

3688886

 

 

 

 

 

captcha