IQNA

Ganawar Ministan Harkokin Wajen Iran Da Shugaban Syria

23:47 - April 16, 2019
Lambar Labari: 3483550
Bangaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da shugaban kasar Syria Basshar Assad yau Talata a birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Bangarorin biyu sun tattauna ne akan yarjejeniyar Astana wacce ta shafi zaman lafiya a kasar Syria, da kuma yarjeniyoyin da kasashen biyu suka cimmawa a lokacin ziyarar da shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad ya kawo nan Iran a watan Febrairu.

Ministan harkokin wajen na Iran ya isa birnin Damascus tare da wata babbar tawagar jami’an diplomasiyya, dake mara masa baya.

Jim kadan bayan isarsa kasar ta Syria, Muhammad Jawad Zarif ya ce; Tattaunawarsa da jami’an gwmanatin Syria za ta mayar da hankali ne akan matakan kiyayya da Amurka take nunawa kasashen biyu.

Daga kasar Syria, Zarif zai wuce zuwa kasar Turkiya domin ganawa da mahukuntan kasar akan batutuwa da dama da suka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma siyasar gabas ta tsakiya.

3804369

 

 

captcha