IQNA

Taro Kan Rawar Da Matasa Musulmi Za Su Taka Domin Ci Gaban Afrika

22:25 - May 09, 2019
Lambar Labari: 3483621
An gudanar da zaman taro na malamai dam asana daga kasashe 27 na Afrika  abirnin kampla na kasar Uganda, kan rawar da matasa musulmi za su iya takawa domin ci gaban Afrika.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar rahoton cewa,a jiya Laraba aka kammala zaman taron malamai dam asana da kuma wakilan kungiyoyin matasa musulmi na kasashen frika a birnin Kamapala fadar mulkin kasar Uganda.

A zaman taron dai an tattauna muhimman lamurra da suke da matukar muhimmanci dangane da irin rawar da matasa musulmi za su iya takawa domin ci gaban nahiyar Afrika baki daya da al’ummominta.

Ali Waisu mataimakin babban malami mai bayar da fatawa na kasar Uganda ya fadi a wajen taron cewa, babban abin da ke da muhimmanci shi ne gina tunain matasa musulmi a  kan himma wajen taimaka wa a dukkanin bangarori na ci gaban al’umma.

Sha’aban Ramadan Mauje babban mai bayar da fatawa na Uganda shi ma a lokacin da yake gabatar da nasa jawabin ya bayyana cwa, bisa la’akari da babbar illar da ‘yan mulkin mallaka suka yi al’ummomin Afrika, na wawushe musu dimbin arzikin da Allah ya huwace wa kasashensu, tare da mayar da su matalauta, ya zama wajibi matasa musulmi na Afrika  su zama a sahun gaba wajen dawo da martabar nahiyarsu.

3810048

 

 

 

captcha