IQNA

23:49 - August 07, 2019
Lambar Labari: 3483922
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da ayyukan hajjia kasar ta ce fiye da maniyyata dubu daya ne za su sauk farali daga kasar.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, kimanin mutane 1310 ne daga kasar Uganda suke halartar aikin hajjin bana a halin yanzu, 900 daga cikinsu babbar majalisar muuslmin kasar ce karkashin sheikh Ramadan Mubaja ta dauki nauyinsu, sauran kuma wasu cibiyoyi na addini kasar.

Yanzu haka dai dukkanin maniyyata an kasar Uganda da aka yi wa rijista sun isa kasar Saudiyya, kuma tuni suka isa birnin Makka domin gudaar da aikin hajjin bana.

Kasar Uganda na daga cikin kasashen gabashin nahiyar Afrika, inda musulmi suke rayuwa a cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakaninsu da sauran mabiya addinai na kasar.

 

3833188

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: