IQNA

23:00 - August 27, 2019
Lambar Labari: 3483991
Jaridar Alnahar ta Lebanon ta bayyana manufar harin Isra’ila a Beirut da cewa ita ce kashe kusa a Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin arabi 21 ya bayar da rahoton cewa a cikin rahoton da jaridar ta buga, ta bayyana cewa, bisa bayanan da ta samu daga wasu majiyoyi na tsaro, sun tabbatar da cewa Isra’ila ta yi nufin kashe wani mamba ne a majalisar dokokin kasar Lebanon dan kungiyar Hizbullah.
Rahoton ya ci gaba da cewa, bisa bayanan da aka samu, Isra’ila ta aike da jirage biyu ne marassa matuki wadanda dukaninsu suna dauke da bama-bamai da nufin aiwatar da wannan ta’asa amma ba ta yi nasara ba.
Daya daga cikin jiragen ya tarwatse tun sama, yayin da daya kuma ya fado, wanda halin yanzu yana a hannun dakarun Hizbullah suna gudanar da bincike a kansa tare da hadin gwiwa da jami’an tsaron Lebanon.
A nasa bangaren shugaban kasar ta Lebanon Micheil Aoun ya bayyana yunkuri da cewa shelata yaki ne a kan Lebanon.

3837908

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Hizbullah ، Lebanon ، harin ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: