IQNA

23:55 - September 30, 2019
Lambar Labari: 3484105
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Amurka sun bukaci da a warware matsalar Kashmir ta hanoyoyi na lumana.

Kamfanin dillancin labaran iqna, musulmin jihar Maryland da ke kasar Amurka, sun bukaci mahukuntan kasar ta Amurka da suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen cin zarafin musulmi a yankin Kashmir ta India.

A cikin bayanin nasu musulmin yakin Maryland sun bakaci da a dauki matakai da za su taimaka wajen ganin gwamnatin kasar India ta kawo karshen takurawa da take yi wa musulmin Kashmir, tare da samo hanyoyi na warware wanann matsala.

Musulmin na jihary Maryland sun yi wannan kira ne a wani zaman taro da suka gudanara babban ofishin cibiyar muuslmi ta kasar Amurka da ke yankin, inda suka gabatar da wannan kira, wanda aka aike ga mahukuntan kasar ta Amurka.

 

3846158

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulmi ، Kashmir ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: