IQNA

23:27 - October 30, 2019
Lambar Labari: 3484205
Jagoran juyin Musulunci a Iran ya shawarci kasashen na Lebanon da Iraki da su fifita warware matsalar tsaro da kasashen ke fama da ita.

Ayatullah Sayyid Ali Khamne’i, ya bayyana hakan nea wajen bukin yaye daliban sojia kwalejin tsaro ta “ Khatamul Anbiya’a” dake nan birnin Tehran da aka gudanar a yau laraba.

Da yake ishara game da abin da ke faruwaa kasashen Irakida Labanon, jagoran ya bayyana cewa Makiya suna kulla makircin haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a wasu kasashen yankin, don haka yanada kyau mahukuntan kasashen su sani cewa warware matsalar tsaro ita ce muhimman abin da ya kamata su fi ba wa fifiko, su ma alummomin kasashen su sani cewa za su iya neman hakkinsu ne kawai karkashin dakokin da tsari ba tare da wani tashin hankali ba.

Har ila yau jagoran ya kara da cewa babbar illa da za’a yi wa wata kasa shi ne a janye zaman lafiya da tsaro da ta ke da shi, don haka ya zama wajibi mahukuntan kasashen su farka game da makiricin da Amurka da wasu cibiyoyin lekan asirin kasashen turai ke kullawa na haifar da rikici da hargisti a wasu kasashen yankin da hadin bakin wasu kasashe a yankin ta hanyar yin amfani da kudade.

Da yake ishara game da muggan laifuffukan da sojojin kasashen Birtaniya ,Amurka Faransa da suka tafka a shekaru 100 da suka gabata a yankin Indiya da kudanci da gabashin Asiya da Arewaci da tsakiyar Afrika , ya nuna cewa babbar matsalar ita ce dogaro da sojojinsu suke yi da wadannan kasashen ne ma’abota girman kai.

Daga karshe jagoran ya jaddada cewa da karfin Allah Zanga- zangar da ake yi ta neman hakkin komawar yan gudun hijira palasdinawa zuwa gidajensu a yankin Gaza , rana za ta zo da wannan burin zai tabbata inda dukkan palasdinawa za su koma gidajensu na asali.

 

3853395

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: